Matasa sun kwashe shinkafa a tsohon gidan wani jami’in gwamnatin Kano

Date:

Rahotanni daga unguwar Gandun albasa da ke karamar hukumar birni a jihar kano, na tabbatar da cewa wasu matasa sun farwa wata makaranta mai suna Wada Sagagi, inda suka kwashi shinkafa mai rubutun gwamnatin tarayya a jikin buhunta.

Wasu mazauna unguwar sun ce, matasan sun shiga gidan ne da talatainin daddare, domin kwasar shinkafar da ake zargin wadda gwamnatin tarayya ta aiko ne domin rabawa mabukata a jihar.

Matsayin Addu’ar kasa “National Prayers” da yan Nigeria za su yi a mahangar shari’ar musulunci – Dr. Ibrahim Iliyasu

Makarantar dai, na zaune ne a tsohon gidan shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kano, Alh Shehu Wada Sagagi.

Duk kokarin da Hikima Radio ta yi domin jin ta bakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Shehu Wada Sagagi da zargin ke alakantawa da kayan, lamarin yaci tura.

Farashin kayan abinci na daf da karyewa a kasuwa — Kwastam

Amma shugaban makarantar Islamiyyar ta Wada Sagagi ya tabbatar da faruwar shigar matasan cikin makarantar tare da kwasar buhunhunan shinkafar.

Idan za a iya tunawa kadaura24 makwani biyu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta ce ta turawa gwamnonin jihohin Nigeria tirela 20 ta Shinkafa zuwa kowacce jiha domin rabawa talakawa don magance matsalolin matsin rayuwa da ake ciki a Nigeria.

Hikima Radio

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...