Daga Sani Idris Maiwaya
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, a ranar Litinin ta sanar da kama wani Ahmed Tela, inda ta ke zarginsa da dinka tutocin kasar Rasha da wasu masu zanga-zanga ke amfani da su a Kano da wasu jihohin Arewa.
An kuma kama masu zanga-zanga kimanin 30 da ke dauke da tutocin tare da tsare su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar ta farin kaya (DSS) a wani taron manema labarai da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya.

Kadaura24 ta ruwaito yadda wasu masu zanga-zangar ke fitowa kan manyan titunan Nigeria musamman jihohin Kano Kaduna Bauchi da wasu jihohin Arewacin Nigeria dauke da tutocin kasar Rasha musamman a wanna rana ta 5 da fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Nigeria.

An ga masu zanga-zangar dauke da tutocin kasar Rasha suna zagaya tituna suna rera wakoki daban-daban tare da wasu dauke da alluna.
Zanga-zanga: Bayan gurfanar da mutane 632, Gwamnan kano ya magantu kan masu daga tutar Rasha
Daily trust ta rawaito da yake jawabi a wajen taron, Adejobi ya ce daga tutocin wasu kasashe a Najeriya, wadda aka kasa ce mai cin gashin kanta, laifi ne, inda ya kara da cewa wadanda aka kama da wadanda suka dauki nauyinsu za a tuhume su kamar yadda dokar kasar ta tanada kan laifukan da suka aikata.
“Da safiyar yau ne muka kama wani ‘Ahmed Tela’ daga karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bisa laifin samar da tutocin kasar Rasha masu yawan gaske da ake baiwa matasan Najeriya domin su dagawa.
“ Mun kama shi, Kuma muna kara farautar wasu musamman wadanda suka sa ka su. Kamar yadda nake magana da ku, haka abin ya faru a Kaduna. mun sami damar kama 30 daga cikinsu dauke da tutocin Rasha ” in ji babban jami’in ‘yan sandan.