KNUPDA ta kafa kwamitin karbar korafe-korafe akan harkokin gine-gine

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Hukumar Tsara Birane ta jihar Kano ta kaddamar da kwamitin da zai fara karbar koken-koken masu korafi dangane da mallakar filaye da gidaje da gonaki har ma da shaguna a fadin Jihar Kano

Shugaban Hukumar Arc. Ibrahim Yakubu Adamu ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin mai mutane biyar karkashin jagorancin Daraktan Mulki na Hukumar Alh Aminu Umar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar KNUPDA Bahijja Malam Kabara ta sanya wa hannu kuma ta aikowa kadaura24.

Talla
Talla

Shugaban Hukumar yace sun lura da cewa abokan huldarsu na kokawa dangane da yadda wasu daga cikin Jami’an hukumar ke amfani da damar da suke da ita tare da yin-sama-da-fadi da sunan hukumar inda su ke aikata ba dai dai ba

Yace kwamitin zai dinga karbar korafe-korafen al’umma a ranakun Litinin zuwa Juma’a, kuma duk wanda aka samu da laifi zai girbi abinda ya shuka bisa tanade tanaden doka.

Gwamnatin Kano ta musanta labarin kashe Naira Biliyan 10 wajen siyan kayan Ofis

Da ya ke Jawabi, shugaban kwamitin Alh Aminu Umar yasha alwashin yin aiki tukuru don magance matsalar da hukumar ke fuskanta, yana mai karin haske da cewar zasu dauki mataki nan take ga duk wadanda suka samu da laifi, tare da gabatarwa Hukumar kundin korafe-korafen da suka karba duk bayan watani shida.

‘Yan kwamitin sun hadar da Aminu Umar a matsayin Shugaba, da Mujtaba Inuwa da Kabiru Musa Dagumawa da Sani Salisu Kabara sai Abubakar Bala a matsayin magatakardar kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi...

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa...

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...