Daga Umar Usman
Majalisar zartaswa ta tarayyar Nigeria a ranar Litinin din nan ta umurci kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da ya sayar da danyen mai ga matatar Dangote da sauran matatun cikin gida da kudin kasar nan naira ba dalar Amurka ba.
Shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta tarayya (FIRS) Zack Adedeji ya bayyana haka bayan taron FEC da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Litinin.
![Talla](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG-20240701-WA0033-2-300x300.jpg)
Adedeji ya ce matakin zai rage radadin kudaden da kasar ke kashewa a kasashen waje tare da daidaita farashin man fetur da dizal da sauran kayayyakin da ake amfani da su a Najeriya.
Rushe Masarautu: Dan Majalisar Tarayya na NNPP Ya Soki Gwamnatin Kano
Adedeji ya ce majalisar zartarwar ta ba da umarnin cewa ba tare da bata lokaci ba hukumar NNPCPL ta fara aiwatar da wannan umarni don bunkasa masana’antun man fetir na gida Najeriya.
Shugaban hukumar tattara kudaden shigar ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta bayar da umarnin matatar Ɗangote ita ma ta sayar da tataccen man ga yan kasuwar mai na gida da naira ba dalar Amurka ba.
Solacebase