Rarara ya Magantu AKan Goge Shafinsa da Facebook Ya Yi

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa ko a jikinsa game da yan Nigeria suka dauka akan sa wanda ya kai ga goge shafinsa na dandalin Facebook.

” Yanzu kana ganin dan na shuka masara ta ta girma wani ko wasu sun zo sun sare ta , shi kenan sai naki sake dasa wata?”.

Dauda Rarara ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta sa’a guda da suka yi da gidan jaridar DCL Hausa.

Talla
Talla

Mawakin ya ce idan an Kan wakar da ya yiwa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne to al’umma su sani yanzu ma ya fara yiwa Tinubu waƙa saboda ya yi abun da ba wani shugaban kasa a Nigeria da ta taba yi.

” Na yiwa Shugaba Bola Tinubu waƙa kuma zan cigaba da yi masa waƙa saboda na gamsu da abun da yake yi na cigaban Nigeria”. Inji Rarara

Yace akwai mutane dawa da suke kaunar wakokinsa don haka bai damu ba don a rufe shafinsa na Facebook, inda ya ce yanzu haka ma ya sake bude wani mai suna Rarara Gallery.

Rushe Masarautu: Dan Majalisar Tarayya na NNPP Ya Soki Gwamnatin Kano

Da aka tambaye shi dalilin da yasa yake yin abubunwan da Ake magana akansa l, Rarara ya ce ” ai ni ko bance komai ba sai an yi maganata, ba a minti daya baka ji muryata ko ka ga hotuna ai ko zagina ne sai ka ji an yi”.

Ya nuna cewa mutane ba su fahimci waƙarsa , saboda a cikin wakar yana cewa Yunwa Gyaram, Talauci Gyaran security daram. Ya ce yana nufin tunda Tinubu ya baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu, to Talauci da yunwa za su kau daga cikin al’umma kuma tsaro ya tabbata , tunda dama talauci da rashin aikin yi ne ya haifar da rashin tsaro a Nigeria.

Talla

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa matasan Arewacin Nigeria sun koka da yadda Rarara ya yiwa Tinubu waƙa a dai-dai lokacin da al’umma suke kokawa da talauci da tsadar rayuwa, wanda hakan yasa jama’a sukai ta kai karar shafin mawakin kuma Facebook suka rufe shafin gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...