Sojoji Sun Gargaɗi Masu Shirin Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Date:

 

Rundunar Tsaron Najeriya ta gargadi masu shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya ta ce sojoji ba za su kyale su su tayar da fitina ba.

Hedikwatar Tsaron ta yi gargadin cewa sojoji ba za su zura ido ga a yi kone-kone da dangoginsu na karya doka da oda da sunan zanga-zangar ba.

Dubban ’yan Najeriya musamman matasa sun ayyana 1 ga watan Agusta da ke a matsayin ranar fara zanga-zangar gama gari ta tsawon kwanaki 10 a fadin kasar kan tsadar rayuwa da ta addabe su.

Talla
Talla

Masu zanga-zangar, mai taken kawo karshe mummunan shugabanci — #EndBadGovernace — sun nuna damuwarsa kan tsananin yunwa da hauhawan farashin kayan masarufi fiye da kima da ake ci gaba da fama da su a kasar.

Amma da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, Daraktan yada labaran Hedikwatar Tsaron, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojoji ba za su zuba ido Najeriya ta fada a cikin yanayin rashin doka da oda ba.

Kungiyar Gwamnonin APC Ta Fadi Matsayarka Kan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa a Nigeria

Manjo-Janar Edward Buba ya ce sojoji sun bankado shirin wasu miyagu na amfani da zanga-zangar domin kawo tashin hankali ta hanyar kai hare-hare kan dukiyoyin al’umma.

Buba ya kara da cewa, “Soji ba za su nade hannu suka kasa ta koma babu bin doka da oda ba.

Talla

“Dalili kuwa shi ne mun ga irin illa da barnar da rashin bin doka suka yi a kasashen da muka gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, muamman a lokacin rundunar ECOMOG ta kungiyar kasashen ECOWAS.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...

Yadda Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgi lokacin yana kan mulki – Garba Shehu

  Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kwamishinan da ya tsayawa wanda ake zargi da harkar kwayoyi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...