Daga Ibrahim Sani Gama
Shugaban Kungiyar yan kasuwa ta AMATA da ke tashar Yankaba ta jaddada aniyarta na dakatar da masu rashin ayyukan yi a cikin Tashar domin dakile shaye-shayen mugwan Kwayoyi a tashar.
Shugaban kungiyar Nasiru Muhammad ne ya jaddada hakan a lokacin da Kungiyar ta yaye wasu Matasa da suka ajiye Makamansu daga harkokin shaye-shaye.
Nasiru Muhammad ya ce bai kamata a rika tsangwamayar yaran da suke aikata laifuka marasa kyau bai, inda yace yin haka yana taka muhimmiyar rawa wajen kara lalacewarsu.

Shugaban Kungiyar ya yi kira gwamnatoci da masu hannu da shuni da su rika zakulo irin wadannan masu aikata laifuka domin neman musu ayyukan yi da su dauke hankulansu da aikata munanan dabi’un da suke aikatawa.
Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Kan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa a Nigeria
A jawabinsa shugaban jami’an sa kai na tashar yankaba Alh. Bala Danyalwa ya ce akwai wani kalubalen da ya kamata gwamnatin karamar hukuma da ta jiha su magance shi, shi ne magance yawon yara Barkatai a tituna da tashoshin mota.
Ya ce akwai yara kusan Dari biyar da su ke kwana a cikin Tashar yankaba wadanda ba’a san daga inda suka fito ba, wanda barazana ga al’umma.

Yace, suna iya kokarinsu wajen mayar da wasu da suka San garuruwan iyayensu da jihohinsu Wanda sun mayar da yara da ba za su kirgu ba zuwa jihohinsu Wanda suna yi ne da aljihunsu.
Ya kuma bayyana cewa, nan gaba kadan Kungiyar za ta sake zakulo wasu Matasan da basu da ayyukan yi tare da basu horo akan sana’oi daban daban da ma basu jari.
Wani daga cikin Matasan da suka amfana da wannan tagomashi Muhammad Auwal sani ya godewa Shugabancin Kungiyar ta AMATA Yankaba, bisa jarin da aka bashi tare da Kayayyakin Wankin Mota domin ya dogara da Kawunansu.
Matashin Auwal sani, ya sha Alwashin yin amfani da Kudaden ta hanyar da suka kamata domin dogaro da kansa kamar yadda aka bukacesu,inda ya bayyana cewa, sun yi mutukar farin ciki tare da yin alkawarin ba za su sake aikata Munanan Dabi’u ba.