Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum ya raba wa dalibansa kyautar kuɗade da kayan abinci.

Rahoton da Aminiya ta samu ya nuna wasu sun samu kwalin taliya da kuɗi, wasu sun samu kuɗi Naira dubu 10, wasu kuma dubu 20, wasu kuma 30 har da waɗan da suka samu sama da haka.
Majalisa Ta Amince Da Kudirin Mafi Ƙarancin Albashin Ma&aikata
“Wannan fa zallar [kyautar] ɗalibai ce aka yi yau.
“Za a yi na mutanen gari [daga bi sani] inda aka tanadi shinkafa da gero da sauran kayan abinci da za a raba wa mutanen gari cikin wannan satin in sha Allahu,” a cewar majiyar.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yan watannin nan mutane suna fama da ƙaranci kudi da kuma tsadar kayan abinchi wanda hakan ya yi sanadiyar mutane suka shiga mawuyacin hali.