Rikicin Masarautun Kano: Yadda Matasa suka hana wakilin Sarki Sanusi shiga gidan sarkin Rano

Date:

Daga Mubina Mahmoud

 

Mazauna Masarautar Rano a ranar Talata sun kori wani mutum da maimartaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya nada domin tafiyar da harkokin masarautar da aka soke har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a kotu kan rikicin masarautun a jihar.

Wakilin ya isa garin ne da safiyar ranar Talatar nan, tare da rakiyar manyan masu rike da mukaman siyasa daga yankin, ciki har da babban mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin makarantu masu zaman kansu, Ibrahim Yaluwa, da kuma shugaban karamar hukumar ta Rano, Dahiru Yakubu.

Sai dai wasu fusatattun matasan garin sun rika jifan ‘yan tawagar jim kadan bayan da jami’an karamar hukumar suka kafa tanti a gaban fadar Sarkin Rano da aka kafa domin wakilin ya samu mubaya’a daga dagatai da masu unguwanni.

Talla

A ranar Larabar nan ne wani mazaunin garin Sabiu Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa an tilasta wa tawagar komawa sakatariyar karamar hukumar da ke karkashin kulawar ‘yan sanda.

“Ya shigo garin ne ta karamar hukumar Kibiya maimakon babban titin Kano,” in ji Ibrahim

Mun Rufe Wurin Sallar Da Aka Mayar Da Shi Gidan Gala a Wudil – Bilkisu Indabo

“Sun garzaya zuwa sakatariyar karamar hukumar, inda ya zauna na dan lokaci kafin DPO na ‘yan sanda su fito da shi.”

‘Matasan sun lalata Mota kirar Prado SUV ta wakilin Ranon, Mannir Abubakar, wanda sarki Sanusi II ya tura.

Wani mazaunin garin Garba Rano, ya Matasan sun kuma lalata ababen hawa na yan jam’iyyar NNPP a karamar hukumar.

Kotu ta sanya ranar da Ganduje da Matarsa zasu bayyana a gabanta

Majiyar kadaura24 ta Premium Times ta ce duk kokarin da ta yi na neman kakakin rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa yaci tura.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito majalisar dokokin jihar kano ta soke dokar masarautun Kano ta shekara ta 2019.

Soke dokar na nufin rusa masarautun da aka kirkiro a 2019 – Bichi, Rano, Gaya, da Karaye .

Daya daga cikin sarakunan da aka tsige, Aminu Ado-Bayero na Kano, na kalubalantar tsige shi a gaban kotu, inda ya koma gidan sarki na Nassarawa GRA.

Premium Times

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...