Rikicin Masarauta: An Samu Tsaiko A Shari’ar Sarautar Kano

Date:

Rashin sadar da sammaci ga wadanda ake kara ya hana sauraron shari’ar rikicin Masarautar Kano da ke gaban babbar kotun jihar Kano a ranar Talata.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano bai samu damar sadar da sammaci ga Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan na masarautun jihar hudun da aka rushe ba.

Masu karar da suka hada da Kwamishinan Shari’a da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar sun shigar da karar ne ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida.

Wata Sabuwa: Sarki Aminu Ado Bayero ya baiwa hakiman Kano Sabon Umarni

Masu karar sun nemi kotu ta hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan hudu da suka hada da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Karaye, Dokta Ibrahim Abubakar ll, da Sarkin Rano Muhammad-Inuwa, da Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya, bayyana kansu a matsayin sarakunan wadancan masarautu da aka rushe.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da Daraktan hukumar DSS da Kwamandan Hukumar Sibil defens da Rundunar Sojin Kasa.

Yayin zaman kotun na yau talata, Lauyan Shugaban ’Yan sanda, Abdussalam Saleh ya shaida wa kotun cewa duk kokarinsu na sadar da sammaci ga wadanda ake kara abin ya ci tura.

Lauyan wadanda ake kara Eyitayo Fatogun SAN, ya nemi kotun ta sa wata rana don su sami damar hada duk wasu bayanai na sammaci ga wadanda ake kara.

Gwamnatin Kano ta tasamma warware rikicin ta da yan jaridun da sukai Mata tawaye

Alkalin kotun, Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta ce ‘ba daidai ba ne wanda ake kara na shida ya ki bayar da sammaci ga wadanda ake kara ba don wai akwai wani umarnin kotu da ya hana a kama ko cin zarafin sarakunan biyar ba.

“Abin da shari’a ta sani shi ne kai za ka ba su sammaci ne kawai, don haka umarnin kotun farko ba zai dakatar da kai daga aikinka ba.

“Ya za a yi ka ba wanda ake kara na farko kariya sannan ka ce ka kasa sadar da sammaci gare shi?”

Mai Shari’a Amina Adamu ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Yuni, 2024.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar 27 ga Mayu kotun ta bayar da umarni ga wadanda ake kara ko ’ya’yansu ko bayinsu su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun don samun dorewar zaman lafiya a Jihar Kano.

Haka kuma kotun ta umarci ofishin Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano da ya sadar da sammaci ga wadanda ake kara.

Daily trust ta rawaito cewa a ranar 23 ga Mayu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sauke dukkanin sabbin masauratun Jihar guda hudu inda shi kuma gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sake nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...