Rikicin masarautu: Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya Magantu a karon farko

Date:

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga al’ummar jihar su kwantar da hankula, yana mai cewa jami’an tsaro na aiki domin tabbatar da tsaron lafiyar jihar.

Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a ƙaramar fadar sarki da ke Nassarawa, Alhaji Aminu Ado ya ce mutane su yi addu’ar samun zaman lafiya.

Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano

”Jama’a a kwantar da hankula, jami’an tsaro na aiki, domin tabbatar da tsaron lafiya”.

Da asubahin yau ne Alhaji Aminu Ado ya koma Kano, kwana biyu bayan gwamnan jihar ya tuɓe shi.

Jami’an Tsaro Sun Bayyana Matsayarsa kan Dambarwar Masarautar Kano

Shi ma kwamishinan ‘yan sandan jihar cikin wani jawabi da ya yi a shalkwatar ‘yan sanda da ke Bompai ya yi kira ga mazauna birnin su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai.

CP Gumel ya ce jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...