Mulkin APC ya mayar da ƴan Najeriya mabarata – PDP

Date:

 

A Najeriya, babbar jam’iyyar hamayya ta kasar, wato PDP, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar ta jam’iyyar APC, game da karin albashin da gwamnatin ta yi, da cewa wani mataki ne na an yi ba a yi ba.

Domin kuwa jam’iyyar PDPn na ganin an yi karin albashin ne yayin da jama’ar Najeriya ke ta fama da matukar tsadar man fetur da tsadar kayan abinci da dai sauran matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa.

A ranar Talata, kwana ɗaya kafin ranar bikin ma’aikata ta duniya ne ofishin kula da albashin ma’aikata na Najeriya ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa an yi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari.

Lamarin ya haifar da cece-ku-ce ganin cewa akwai wani kwamiti da gwamnatin ta kafa wanda aka ɗora wa alhakin samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar.

Tinubu ya karawa ma’aikatan Nigeria albashi

A tattaunawarsa da BBC, Ibrahim Abdullahi, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na jam’iyar na kasa ya ce, halin da Najeriya ta shiga a ƙarƙashin mulkin APC cikin shekaru tara, ya sanya ƴan ƙasar sun koma mabarata saboda yunwa “Ana fuskantar mummunan rashin tsaro da halin ha’ula’i da ƙasa ta shiga.”

Jam’iyyar ta PDP na ganin ko da an yi ƙarin albashi, adadin ƙarin ba zai samar da maslaha ba a cikin halin ƙunci da kariyar tattalin arziƙi da suke ciki ba.

Zargin Rashawa: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta ba da shawarar Cire MD ARTV

“Abin da shi ma’aikaci yake tunanin zai samu shi ne sauƙi, ba kawai a ƙara albashi cikin mummunan hali ba saboda ƙarin ba ya iya saya masa kashi goma na abin da a baya yake iya saye, domin haka wannan shi ne ci gaban mai shiga rijiya.”

Ibrahim Abdullahi, ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar da tsaro ga manoma domin su noma abincin da ƙasa za ta samu ya wadata domin a samu sauƙin abincin.

PDP ta ce janye tallafin man fetur na kan gaba wajen haifar da halin da Najeriya ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...