Daga Halima Musa Sabaru
Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau alhamis 02-05-2024 za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 42 bisa ma’aunin zafi.
Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.
Mulkin APC ya mayar da ƴan Najeriya mabarata -PDP
Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai Sauya zuwa 40 zuwa 41 zuwa 42 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.
Zargin Rashawa: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta ba da shawarar Cire MD ARTV
Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.
Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen goben zai kasance