Daga Hafsat Lawan Sheka
Kamfanin Man Fetur na Najeriya ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai kawo karshen matsalar karancin man fetur da layukan da ake yi a ranar Laraba 1 ga watan Mayu.
Mista Olufemi Soneye, shugaban sashin hulda da jama’a na kanfanin NNPC ne ya bayyana hakan ga kanfanin Dillancin Labara na kasa ranar Talata a Legas.
A cewar Soneye, kamfanin a halin yanzu yana samar da man fetur din da ya wuce lita biliyan 1.5, wadanda zai iya kaiwa akalla kwanaki 30.
Gaskiyar Magana Game da Dawo da Tallafin man fetur a Nigeria
“Abin takaici, mun samu cikas na tsawon kwanaki uku saboda wasu dalilai, amma mun shawo kan matsalar.
“Kamar yadda kuka sani, shawo kan irin wannan matsalar indai ta Faru tana daukar lokaci mai Tsawon, amma dai yanzu komai zai koma yadda yake nan da ranar 1 ga watan mayu na wannan shekarar,” in ji shi.
Ya ce: “Wasu mutane suna amfani da wannan yanayin don haɓaka ribar da suke samu
“Za a magance layukan man da Ake ganin tsakanin yau da gobe,” in ji Soneye.