Daga Alkasim Muhammad Nasir
Al’ummar unguwar Kadawa Mil-tara dake karamar hukumar ungoggo, sun karrama wani jami’in dan sanda mai suna Inspector Detective Aminu Sulaiman jikamshi da kambar girmamawa bisa gudunnawar da yake bayarwa wajen gano masu aikata daban-daban.
Shugaban Kungiyar cigaba unguwar Dr.Abubakar Isah Tumfafi ne ya jagoranci bikin karramawar da aka yiwa dan sandan yayin wata Liyafar da aka shiryawa Detective Aminu sulaiman jikamshi .
Dan sandan yana aiki ne a sashin bincike da gano masu aikata Manyan laifuka a Rundunar yan sandan jihar Kano.
Zargin Almundahana: NAWOJ ta Bayyana Matsayarta Kan Rikicin da NUJ da RATTAWU Ke Yi da MD na ARTV
Ditective Aminu Sulaiman na daga cikin yan sanda da a Ranar 15 ga watan nan da muke ciki Bababn Sifetan Yan Sandan Nigeria Kayode Egbetokun ya karamma saboda aikin da suke tukuru.
Akarshe Kungiyar Kadawa New Layout Development Association Mil-Tara ta Kuma ya bawa Rundunar Yan Sanda ta kasa ta karrama Dansu.