Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Matashiyar nan da shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ya yiwa waƙar Fatima Mai Zogale ta yi karin haske kan yadda akai mawakin ya yi mata waka.
” Dama ni na Kasance Ina kaunar wakokin Rarara, hakan tasa nake bibiyar duk wakokin da yayi, kwacham wata rana sai ga mawaki Rarara a inda muke sayar da Zogale a cikin Yahuza Suya dake Abuja”.
Fatima Mai Zogale dai ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da Kadaura24 ta ci karo da shi a shafukan sada, Inda tace mayar da martani kan yadda uwar dakin ta tace bata koreta daga Aiki ba.
Hukumar NEMA ta Bayyana Adadin Wadanda Suka Rasu a Hatsarin Ginin da Afkawa wasu a Kano
” Rarara ya zo wurin da muke siyar da zogale a Abuja ya siya zogale. Daga ganin sa sai na kiɗime na ce yau gani ga Rarara, ya siya Zogale ya kuma tambayi suna na, sannan suka tafi.
Tace bayan kwana biyu da siyan zogale a wurin kawai sai aka zo aka fada min cewa Rarara fa ya yi min waƙa mai suna Fatima Mai Zogale, to da yake bani da Babbar waya sai nasa a kunna min waƙar kuma na ji ta yi dadi sasai.
” Daga nan sai wacce na ke wa aiki ta ce ita ce mai wuri, ba a yi mata waka ba sai ni yar aikin,to ban isa ba, daga nan sai ta tace na bar mata wajen ta, na bata hakuri amma taki hakura ta dage sai na bar mata wurin siyar da Zogalenta.
Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano
Sai dai bayan haka uwar ɗakin Fati Mai zogale ta fito cikin wani bidiyo a ranar juma’a ta na karyata cewa wai ta kori Fati Mai Zogale daga bakin aiki.
“Sai dai Fatin ta ce shirga karya ta yi, ba yanzu ta taba korar ta bayan sun ɗan samu saɓani wurin siyar da Zogale.
Wakar Fatinmai Zogale dai ya karaɗe shafukan sada zumunta da wasu gdajen radiyo inda ake saka wa ana ji don nishaɗi