Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi gyaran fuskanta ga majalisar zartarwar gwamnatin jihar kano, domin inganta aiki da cigaban jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ya aikowa kadaura24 a ranar Alhamis, yace an jaddada cewa wadannan gyare-gyaren wani bangare ne na jajircewar Gwamna Yusuf na inganta harkokin mulki.
Kotu Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje
Daga cikin wadanda sauye-sauyen ya shafa akwai Mustapha Rabi’u Kwankwaso, wanda aka nada shi a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, Hajiya Amina Abdullahi, wadda aka mayar da ita daga ma’aikatar aiyuka ta musamman zuwa sabuwar ma’aikatar agaji da yaki da fatara da aka kafa. Alhaji Abbas Sani Abbas, wanda aka mayar da shi daga ma’aikatar kasuwanci, da zuba jari zuwa ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma.
Gwamnan Kano ya Bayyana Ma’aikatun da aka tura Sabbin Kwamishinonin a jihar
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Hon. Hamza Safiyanu Kachako, tsohon Kwamishinan Raya Karkara, za a tura shi wata ma’aikatar nan gaba .
Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, daya daga cikin sabbin kwamishinonin da aka rantsar, an nada shi ya jagoranci ma’aikatar kasuwanci, ciniki da zuba jari.
Gwamna Yusuf ya bukaci wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu cikin himma da sanin ya kamata domin bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar gudanar da gwamnati baki daya.