Daga Ibrahim Sani Gama
Shugaban Kungiyar Masu hada-hadar kudaden canji ta kasashen waje dake jihar Kano, Alhaji Sani Dada ya bayyana jin dadinsa bisa yadda gwamnatin tarayya take kara karya farashin dala kowanne lokaci a kasar.
Kadaura24 ta rawaito Alhaji Sani Dada ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake kasuwar canji ta Wapa, Kano.
Yace rage farashin kudaden waje da babban bankin Kasa yayi, zai fitar da masu hada-hadar canji daga zarge zargen al’umma na cewa sune suke da alhakin tashin gwauran zabin da kayayyakin masarufi suke yi a Kasuwannin Nigeria.
Yanzu-yanzu: CBN Ya Sake Karya Farashin Dala a Nigeria
Shugaban yace wannan kalubale na tsadar kayayyakin masarufi yanzu ya rage tsakanin yan kasuwa da al’ummar Kasar, saboda yanzu jama’a za su fahinci inda gizo yake saka.
” A baya Mutane sun zage mu mun dora mana alhakin tashin Dala Wanda kuma muma bamu da katabus a kai, amma saboda rashin fahimta mutane suka rika Kalubalantar mu har da dora mana alhakin tashin farashin Kayan masarufi”. Inji shi
Halin da Ake Ciki Game da Neman Watan Sallah Karama a Saudiyya
Sani Dada yace kungiyar masu hada hadar canji ta Wapa, ta himmatu wajen ganin an kara inganta rayuwar matasa musamman, ‘ya’yan Kungiyar masu hada hadar canji domin rage marasa ayyukan yi da kuma farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Daga karshe Shugaban ya bayyana cewa, Kungiyarsa a shirye take wajen baiwa Gwamnati cikakken hadin kai domin ciyar da jihar Kano da ma Kasa baki daya.