Daga Hafsat Lawan Sheka
Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta tabbatar da cewa ba a sami ganin jinjirin watan Shawwal ba wato watan karamar Sallah a Nigeria.
KADAURA24 ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa Sakataren kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi Farfesa Wali Junaidu ta sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Sokoto .
Yanzu-yanzu: Ba a ga jinjirin watan Karamar Sallah a Kasar Saudiyya ba, Dalili
Sanarwar ta ce al’ummar musulmin Nigeria zasu Cika Azumi guda 30 a bana, don haka ya bukaci al’ummar musulmi su dauki Azumin gobe talata.
Sanarwar tace Laraba 10 ga watan afirilu 2024 shi ne ita ce zata Kasance 1 ga watan Shawwal 1445.
Sarkin Musulmi ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi ibadu da addu’o’in da al’ummar musulmi Nigeria suka yi a cikin wannan wata na Ramadan.