Daga Halima Musa Sabaru
Gwamnan jihar jigawa Malam Umar A Namadi, ya dakatar da kwamishinan ma’aikatar Kasuwanci ta jihar Alhaji Aminu Kanta daga mukaminsa har zuwa lokacin da za’a kammala gudanar da bincike kan shirin ciyarwar buda baki a karamar hukumar Babura.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim.
Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kudirin gwamnati na tabbatar da bin diddigin kudi da kuma tafiyar da kudaden gwamnati yadda ya dace.
Ganduje ya yi martani kan gwamnatin Kano bisa gurfanar da shi a gaban Kotu
Ya ce an dakatar da Kwamishinan ne bisa zarginsa da hannu wajen karkatar da kudaden ciyarwar buda baki a karamar hukumar Babura.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Ofishin Sakataren gwamnatin jihar Ismail Ibrahim Dutse ya fitar, yace dakatarwar ta fara aiki ne nan take tare .