Fitaccen mawaƙi kuma furodusa, Jonathan H. Smith wanda aka fi sani da Lil Jon, ya karɓi addinin Musulunci a wani masallacin garin Culver da ke Jihar California a kasar Amurka.
Kafofin watsa labarai irinsu Daily Sabah da HipHopDx sun ruwaito cewa, a ranar Juma’a Lil Jon ya ziyarci masallacin Sarki Fahad da ke birnin Los Angeles inda ya bayyana cewa ya musulunta a gaban babban taron jama’a.
Gwamnatin tarayya ta bayyana adadin likitocin dake duba lafiyar yan Nigeria sama da miliyan 200
Wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna mawakin yana karanta shahada da larabci sannan da turanci, karkashin jagorancin limamin masallacin.
Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano
Lil Jon wanda aka haifa a shekarar 1972 a garin Atlanta na Jihar Jojiya, shahararren mawaƙin rap ne saboda rawar da ya taka a matsayin jagaba wajen haɓaka rukunin hip-hop a farkon shekarun 2000.
Lil Jon wanda ke da mabiya fiye da miliyan 1 a dandalan sada zumunta, a baya bayan nan ya sake daukar hankalin jama’a bayan fitowar kundin wakokinsa mai suna Meditation .
Bayan marubuci Ba’amurke kuma mai fafutuka Shaun King, Lil Jon ya zama shahararren Ba’amurke na biyu da ya karɓi Musulunci a makon farko na watan Ramadan.