Gwamnatin tarayya ta bayyana adadin likitocin dake duba lafiyar yan Nigeria sama da miliyan 200

Date:

Ministan lafiya da walwalar al’umma a Nigeria, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya nuna damuwarsa kan yadda likitocin Nijeriya suke sulalewa su na fita zuwa kasashen waje.

Ya misalta da cewa abun damuwa inda likitoci masu lasisi guda dubu 55,000 kacal ne ke kula da lafiyar illahirin al’umman da suka zarce miliyan 200.

Ministan wanda ke magana a hirarsa da wani gidan talabijin, ya ce sama da likitoci 16,000 ne suka sanya kafa suka fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da wasu kari su 17,000 aka musu sauyin wajen aiki.

Kotu ta yanke hukunci kan batun nada kantomomi da gwamnan kano yayi

Farfesa Pate ya lura kan cewa ficewar likitoci, jami’an kiwon lafiya da sauran kwararru a wasu fannoni domin zuwa kasashen waje amsar ayyuka masu gwabi, yayin da kasar nan kuma take dan amfani da sauran wadanda suka rage.

A cewarsa, Nijeriya tana da sama da kwararru a bangaren kiwon lafiya sama da 300,000 da suka hada da likitoci, nas-nas, unguzoma, kwararru a bangaren harhada maguna, masu gwaje-gwajen kimiyya da sauransu.

Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano

Ya ce, “Mun gudanar da bincike inda muka gano cewa muna da likitoci masu rajista a Nijeriya guda 85,000 zuwa 90,000. Sai dai ba dukkaninsu ke cikin kasar ba.

“Wasu daga cikinsu sun tafi kasashen ketare, musamman Amurka da Burtaniya. Amma, muna da likitoci masu rajista 55,000 a kasar nan.”

Ya ce hatta wasu ‘yan matsaloli da ake samu a bangaren kiwon lafiya na da nasaba da rashin wadatattun jami’an kiwon lafiyar ne, inda ya nuna matukar damuwarsa kan hakan.

A cewarsa, ba daidai ba ne Nijeriya ta ci gaba da rasa hazikan ma’aikatanta, musamman likitoci ga kasashen waje, ya nuna cewa an fi tsananin bukatar su a nan gida Nijeriya.

 

Leadership

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...