Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Sabon mataimakin shugaban hukumar kwashe shara ta jihar kano Mukhtar Lamin Hassan yace zasu yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsafta a jihar kano duba gudunnawar da gwamnati ke baiwa hukumar karkashin jagorancin Haruna Danzago
Mukhtar Lamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake ziyartar wasu guraren da ake kwashe shara a kano domin sanya ido kan yadda aikin ke gudana.
Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano
Lamin Hassan yace ” yazama dole mu yabawa shugaban wanann Hukuma Haruna Dan zago duba da tun bayan kasantuwarsa a shugabancin yake bijiro da aikace-aikace tare da bin lungu da sako domin tabbatar da tsaftarsu, Hakika ina yabawa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabiru yusuf bisa duba can cantata da ya duba ya nadani a wannan matsayi”.
Har yanzu Nijar taki Bude Bodarta da Nigeria
Yace zai yi duk mai yiwuwa ya bada tasa gudunnawar domin sauke nauyin da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya dora musu na tsaftace jihar kano daga duk wata shara.
Daga karshe yayi kira ga ma’aikatan Hukumar dasu bashi goyan baya domin cigaba da gudanar da ayyukan da zasu kawo cigaba ga Al’umma.