Har yanzu Nijar taki Bude Bodarta da Nigeria

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Sa’o’ 72 bayan da Nigeria ta sanar da bude bodar kasar da jamhoriyar Nijar, har yanzu Nijar ta ki bude tata bodar dake tsakaninta da Nigeria domin cigaba da harkokin mu’amala ta yau da kullum .

Jaridar Daily trust ta rawaito har ya zuwa yanzu dai hukumomin Jamhuriyar Nijar din ba su ce uffan ba game da wannan mataki na gwamnatin Nijeriya.

Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano

Hukumomin Nijeriya irinsu na Kwastam da na kula da shige da fice na Immigration, sun sassauta hanyoyin shiga da fitar, amma na Jamhuriyar Nijar ba su yi hakan ba.

A ranar 13 ga watan Maris din nan dai ne fadar shugaban Nijeriya ta sanar da bude iyakokin kasa da na sararin samaniya ga Jamhuriyar Nijar tare da janye mata takunkuman da aka kakaba mata tun bayan da aka samu samu juyin mulki da ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin kasar ta jamhoriyar Nijar basu sanar da dalilin su na kin bude tasu bodar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...