Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (Rtd) a matsayin Babban Sakataren Hukumar kula da Almajiri da yaran da basa zuwa makarantar ta kasa.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito awanni kadan kafin saukar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari daga mulkin Nigeria ya nada Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin shugaban hukumar.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Alhaji Tijjani Hashim Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Hasken Kan Umarnin Bude Bodar Nigeria da Nijar

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Janar Ja’afar Isa jagora ne nagari ya kuma taba zama gwamnan jihar Kaduna da kakin soji daga 1993 zuwa 1996, yayin da Alhaji Tijani Hashim Abbas shi ne Sarkin Sudan Kano.

Kotu ta yanke hukunci kan batun nada kantomomi da gwamnan kano yayi

Shugaban ƙasar ya yi hasashen cewa sabbin wadanda aka nada din za su yi amfani da gogewar da suke da ita wajen gudanar da aiyukan da aka dora musu don cigaban al’ummar Nigeria.

Lawan Jafaru Isa da Alhaji Tijjani Hashin Abbas dukkaninsu sun fito ne daga jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...