Daga Samira Hassan
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da rage sa’o’in aikin gwamnati saboda shigowar watan Ramadan.
Amincewar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na ofishin shugaban ma’aikata na jihar Alhassan Sule Mamudo ya fitar kuma ya rabawa manema labarai.
Kotu ta yanke hukunci kan batun nada kantomomi da gwamnan kano yayi
Sanarwar ta ce, a yanzu ma’aikatan gwamnati za su fara aiki ne daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana, tun daga Litinin zuwa Alhamis, yayin da a ranar Juma’a kuma lokacin aikin ya fara daga karfe 8:00 na safe zuwa 12:00 na rana.
Sanarwar tace wannan rage lokacin ya shafi watan Ramadan ne kawai kuma za’a koma yadda aka saba bayan watan Ramadan,” in ji Sanarwar