Hukumar mu zata farfado da kima da tattalin arzikin Nigeria – Ali Nuhu

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Sabon Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nigeria Ali Nuhu ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don farfado da kima da mutuncin masana’antar Fina-finai a Nigeria domin ta yi gogayya da takwarorinta na Duniya.

Dr. Ali Nuhu ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi bayan karbar ragamar mulkin hukumar, a matsayin shugaban hukumar na bakwai a Jos dake jihar filato.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na hukumar Brian Etuk ya aikowa kadaura24, yace Dr. Ali Nuhu ya ce ya kuduri aniyar yin amfani da dimbin gogewar da ya ke da ita wajen inganta hukumar dama masana’antun fina-finai dake Najeriya.

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Sa a Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar

Sabon shugaban hukumar ta NFC ya jaddada fatan gwamnatin tarayya da na hukumar fina-finai da sauran masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Nijeriya kan rawar da ya kamata hukumar ta taka wajen farfado da kimar Nigeria a idanun duniya, ta yadda kasar zata zama abar so a zo gani a duniya kamar yadda yan Nigeria suke sha’awar zuwa wasu kasashen.

Dr. Nuhu ya bayyana matukar godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa nadi a wannan mukami, sannan ya yaba wa ministar Fasaha da al’adu ta Nigeria Barr. Hannatu Musawa kuma ya yi alkawarin tallafa wa manufofin Ministar na bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta fuskar fannin fina-finai.

Ramadan: Bayan Hisbah ta Kano Ta Kama Su, Wasu Matasa Sun Bayyana Dalilansu Na Kin Yin Azumi

Da yake jawabi tun da farko, Mista Edmund Peters, Darakta a hukumar, ya ce Hukumar ta samu gagarumar nasara tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1979. Ya bayyana kwarin gwiwar hukumar Gudanarwa da Ma’aikatan hukumar suke da shi akan Ali Nuhu, sannan yayi alkawarin zasu baiwa sabon shugaban hadin kai don ya sami nasarar daga darajar hukumar.

Manyan baki da suka halarci taron sun hada da Alhaji Abba El-Mustapha – Babban Darakta na Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Barr. Ezra Jinang SSA – Kirkira & Nishadantarwa ga Gwamnan Jihar Filato, Alhaji Sani Muazu, fitaccen jarumin Kannywood, da dai sauran masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...