Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da Sanata Abdul Ningi bisa zargin shugabancin majalisar da cushen 3.7trl a kasafin kuɗin shekara ta 2024.
An dakatar da Ningi wanda ya ke wakiltar shiyyar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar Hatsaniya da ta kaure a zauren majalisar.
Wani mamba a kwamitin kasafin kudi a majalisar dattawa, Jimoh Ibrahim, ya fara gabatar da kudirin dakatar da Ningi na tsawon watanni 12 bisa zargin rashin bada bayanai da kuma kawo tsaiko a majalisar dokokin kasar.
Sai dai sauran ‘yan majalisar kamar Sanata Asuquo Ekpenyong sun nemi a yi wa gudirin Ibrahim din gyaran fuska. Ekpenyong, wanda ya fito daga gundumar Cross River ta Kudu, ya roki a rage yawan lokacin dakatarwar.