Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mace ta biyu da ta rike shugabancin karamar hukuma a Kano Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta yi alkawarin fitar da matan jihar kano kunya ta hanyar gudanar da aiyukan da zasu inganta rayuwar al’ummar da take jagoranta.
Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ita ce mace daya da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya nada ta a matsayin shugabar riko ta karamar hukumar Wudil dake jihar.
A zantawarta da manema labarai Bilkisu Yakubu tace ta San akwai kalubale a gabanta a matsayin ta mace ta farko kuma mace guda da aka nada matsayin shugabar riko ta karamar hukumar, sai dai tace ta shirya sosai domin tunkarar wannan kalubale.
Abin da masu amfani da soshiyal midiya za su ƙaurace wa lokacin azumi
” Tabbatas abun da Maza zasu yi Mata ba zasu iya ba, Amma izinin Allah subhanahu wata’ala zan wannan kallabin da ke tsakanin rawuna zai Bada mamaki, domin nayi Shirin na musamman domin ganin ban baiwa mata kunya ba”.
Buhari ya bukaci yan Nigeria su cigaba da hakuri da manufofin gwamnatin Tinubu
Tace zata tsaya tsayin daka domin gudanar da aiyukan raya kasa da cigaban al’ummar karamar hukumar Wudil, inda tace zata fi mai da hankali wajen inganta harkokin ilimi domin da Ilimi ne za’a iya samun nagartacciyar al’umma wadda za’a yi alfahari da ita.
” Kwankwaso ne ya dauki nayin karatu na tun daga Digiri na farko har zuwa na uku kuma ilimin da nayi shi ya bani damar zawa wannan matakin, don haka nima zan dabbaka wannan sunnar ta jagoranmu Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso don Gina al’ummar karamar hukumar Wudil”.
“Ba zan bai wa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kunya ba, kuma suma mata ba zan basu kunya ba, zan yi abun da zai sa daga kaina mata zasu rika samun manyan mukami a Kano da izinin Allah”. in ji Bilkisu Yakubu Indabo, matashiyar da gwamnan Kano ya nada shugabar karamar hukumar Wudil ta riko
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ita ce mace ta biyu da aka taba baiwa rokin kantoma a jihar kano, Inda mace ta farko Fatima Muhammad aka bata kantoma a karamar hukumar Nasarawa.