Ramadan: Abdulmumini Kofa ya raba kayan abinchi da kuɗi na Miliyan 100 ga al’ummar Kiru da Bebeji

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), a ranar Asabar, ya ƙaddamar da rabon kayan abinci da kuɗi kamar yadda ya saba yi a kowane watan azumin ramadan.

Akalla mutane dubu 10 ne suka amfana da tallafin kayan abinchi da kuɗi, kuma an zabo su ne a lungu da sako na kananan hukumomin kiru da bebeji.

Dan majalisar tarayyar yace kayan abinchin da kuɗin da aka rabawa mutanen da yake wakilta sun Kai akalla Naira Miliyan 100.

Yadda Mace ta Farko da Gwamnan Kano Ya Baiwa Kantoma Ta Sha Alwashi

An dai fara rabon ne tun da safe har zuwa tsakar daren Asabar ɗin, kuma a ranar Lahadi ma an ci gaba da rabon ga malaman makaranta, ma’aikatan lafiya, Hakimai, Dagattai, limamai, malamai, marayu, masu buƙata ta musamman, mabuƙa, mata, matasa da sauran ƙungiyoyin jama’a.

Da yake gabatar da jawabi a wajen rabon kayan abinchin Hon. Abdulmumini Jibril Kofa yace ya rabawa mutanesa kayan abinchin ne don saukaka musu sakamakon mawuyacin halin da al’umma suke ciki.

” Dama dai duk shekara Muna rabawa mutane irin wannan kayan, Amma na bana na musamman ne shi yasa muka kara akan abun da muka saba yi duk shekara, saboda halin kuncin da al’umma suke ciki”.

Gwamnan Kano Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Bukaci Tinubu Ya Bude Boda

Ɗan majalisar ya roki mutanen da suka amfana da tallafin da su yi amfani da watan na ramadan wajen yin addu’o’i na musamman ga jihar kano da Nigeria baki daya ko Allah ya Dldubi al’umma ya fitar da su daga wannan hali.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin kayan abinchin da Kudade sun yawaba Kofa saboda yadda ako da yaushe yake kokarin tallafawa al’ummarsa.

Ga hotunan yadda rabon kayan ya Kasance:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...