Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya roki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta duba batun bude iyakokin kasar nan domin samun damar shigo da kayan abinci daga kasashen waje domin rage radadin da talakan Najeriya suke ciki.
Wannan roko na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar jim kadan bayan gwamnan ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam na Najeriya Alhaji Bashir Adewale Adeniyi a gidan gwamnati dake Kano.
Gwamna Yusuf ya koka kan halin da ake ciki na yunwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a Nigeria.
“Muna yabawa shugaban kasa kan shirinsa na samar da abinci a Nigeria, wanda ya dauki Kano a matsayin inda za a kaddamar da shirin, gwamnan yace shirin zai magance matsalar karancin abinci a Nigeria baki daya .”
Yadda Kalaman Abba Hikima akan Gwamnatin Kano suka tada kura a dandalin sada zumunta
A cewar Gwamnan, wani matakin gaggawa da zai iya samar da abinci da araha ga al’umma shi ne gwamnatin tarayya ta duba batun sake bude iyakokin kasar tare da ba da damar shigo da kayayyakin abinchi ba tare da biyan haraji ba.
A yayin ganawarsa da Kwanturolan Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, a ofishinsa, Gwamna Yusuf ya jaddada irin wahalhalun da al’umma ke fuskanta musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda ya jaddada wajibcin bude iyakokin domin rage musu radadin halin da suke ciki.
Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Matan Kano 1,028 tallafi
Ya kuma bayyana jin dadinsa da shirin hukumar kwastam na fara rabon kayan abinci ga al’ummar Kano saboda halin kunci da yunwa da jama’a ke ciki, inda ya bukaci hukumar ta kwastam ta tabbatar da ganin wannan aikin alheri ya kai ga masu karamin karfi .
Bugu da kari, gwamnan ya baiwa hukumar kwastam tabbacin goyon bayansa ba tare da wata tangarda ba ta kowane fanni.
A nasa jawabin, Adeniyi ya nanata mahimmancin karfafa dankon zumunci tsakanin hukumar kwastam ta Najeriya da al’ummar Kano, yana mai jaddada kokarin hukumar wajen yin hadin gwiwa da fahimtar juna.
Ya yi alkawarin aiwatar da tsare-tsare da nufin inganta harkokin kasuwanci da kyautata alaka da masu ruwa da tsaki a jihar.
Adeniyi ya kuma bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin tunkarar kalubalen karancin abinci da wahalhalun da ake fuskanta a Kano ta hanyar raba muhimman kayayyakin abinci ga mazauna jihar.