Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin tallafawa mata 1,028 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 .
Shirin tallafawa matan an yi shi ne da nufin karfafawa mata gwiwa ta fannin tattalin arziki da kuma dogaro da kai, gwamnan ya bada tallafin ne a wani bangare na bikin ranar mata ta duniya, wadda ake yi a duniya a ranar 8 ga Maris.
Yadda Gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan agundi dake Kano
Yayin da yake halartar taron cin abincin rana a gidan gwamnati, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa tallafin kudi an yi shi ne musamman domin baiwa mata damar tsayawa da kafafunsu.
“Muna son matanmu su bunkasa ta fuskar tattalin arziki kuma su kasance masu dogaro da kansu,” in ji shi.
Karancin Ruwa: Gwamna Buni Ya Bada Umarnin Kai Disel A Rijiyoyin Burtsatse A Yobe
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa shirin za a cigaba da bada tallafin lokaci zuwa lokaci.
“A kowane wata, za mu ci gaba da ba matan Kano tallafin ,” in ji shi.
Yace baiwa matan wannan tallafi ya nuna cewa gwamnatin kano bata nuna wariya ba wajen inganta tattalin arzikin al’ummar jihar.