Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu na taka rawar gani tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin kasar a hannun sa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Yayin da wasu daga cikin manufofin shugaban kasa, musamman cire tallafin man fetur da rage darajar Naira da hauhawar farashin kayan abinchi da tabarbarewar tattalin arziki,suka sa yan kasar a cikin mawuyacin hali, amma Buhari ya ce mulkin Najeriya aiki ne mai wahala ga kowa kuma Tinubu yana matukar kokari.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya karbi bakuncin babban kwanturolan hukumar Kwastam a garin Daura na jihar Katsina.
Ramadan: Dan Majalisar Bichi ya kaddamar da rabon Abinchin da ba’a taba yin irinsa ba a Kano
Ya roki ‘yan Najeriya da su jure wa matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a kasar nan tare da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci a yanzu.
“Na gode kwarai da zuwan ku. Na yaba sosai. Ina tsammanin Tinubu yana yi abun a yaba masa sosai, Najeriya tana da sarkakiya sosai. Hakika, babu abin da wani zai iya yi. ” Inji Buhari
Yadda Gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan agundi dake Kano
A nasa bangaren, Bashir Adeniyi, babban kwanturolan hukumar kwastam, ya yabawa tsohon shugaban kasar bisa “canza fasalin hukumar NCS” a lokacin da yake kan karagar mulki.
Adeniyi ya ce, hukumar za ta ci gaba da tabbatar da cewa iyakokin kasar nan sun tabbata domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.