Yadda za ku kula da kanku a lokacin azumin Ramadan

Date:

A cikin watan Ramadan mai alfarma, musulmai a sassan duniya su na azumi, abin da ke nufin ba su cin abinci da rana. Kuma azumin na daya daga cikin shika-shikan Addinin Musulunci.

Domin tabbatar da ganin ba a shiga mawuyacin hali ba a yayin da ake kamewa daga cin abinci da shan ruwa, yana da muhimmanci a kula da abubuwan da ake ci kafin azumin da kuma a cikin Ramadan.

Ya na da kyau a yi sahur da abinci mai sanya kuzari. A lokacin bude baki kuma, yana da muhimmanci a ci abinci mai lafiya, a kuma guji cin abincin da ke da gishiri sosai.

Abubuwan lura idan ana azumi

Mutane masu koshin lafiya ba su da wata matsala a lokacin azumi, amma masu fama da cututtuka suna iya fuskantar cikas. Tunda dai azumi yana shafar hawa da saukar jinin masu ciwon suga, zai iya zama abu mai hatsari ga masu irin wannan ciwo.

Saboda haka ya kamata duk musulmin da ke fama da ciwon suga ya tuntubi likita kafin a fara azumin watan Ramadan.

Wasu mutanen suna fama da gajiya da ciwon kai da kuma jiri da rana. Wannan kuma abu ne da aka fi alakantawa da rashin yin sahur.

Yana da kyau a kula da ingancin abincin da ake ci kowanne lokaci, amma wannan kula ta fi muhimmanci a lokacin azumin Ramadan.

Ya ake tsara abubuwa a cikin Ramadan?

Ya na da kyau a fahimci cewa dadewa da ake yi babu shan ruwa saboda ana azumi yana haifar da karancin ruwa a jikin mutum. Domin kauce wa shiga wannan yanayi ya na da muhimmanci a sha ruwa sosai a cikin dare.

Wani kuskure da ake yi shi ne na kin yin sahur saboda kwadayin samun wadataccen bacci. Idan aka yi sahur da kyau za a iya kauce wa matsalar rashin kuzari da ciwon kai da kuma yunwa da ake fama da su da rana.

Ya kamata abincin sahur ya kunshi na’uin abinci mai gina jiki da mai maiko da kuma mai sanya kuzari. Wannan hadin yana taimakawa wajen daidaita suga a jinin mutum da kuma bai wa jiki kuzarin da ake bukata.

Da me ake yin bude baki?

A lokacin bude baki, akwai bukatar mutum ya yi abin da zai dawo masa da kuzari. Wata dadaddiyar al’ada mi kyau ita ce ta yin bude baki da dabino, kodai a kora da ruwa ko kuma madara wanda hadi ne mai kyau da ya kunshi suga da abinci mai gina jiki da kuma ruwa.

Al’ummar musulmi a sassan duniya suna da al’adar cin abinci mai miya bayan bude baki a lokacin azumin Ramadan. Wannan zabi ne mai kyau da ke taimakawa wajen mayar da abubuwan da jiki ya rasa da rana, kamar abubuwa masu sanya kuzari da ganyaye da kuma hatsi.

A al’adar jama’ar kudancin Asia, mutane suna bude baki ne da ‘ya’yan itace kuma hanya ce mai kyau ta dawo da kuzari da ruwan da jiki ya rasa a lokacin azumi.

Abincin bude baki a lokacin azumin

Ramadan ya na daukar salo irin na biki, inda a lokuta da dama jama’a ke taruwa da ‘yan’uwa da abokan arziki domin cin abincin.

Sai dai ya na da kyau a tuna cewa cin abinci mai maiko sosai zai sa mutum ya yi fama da kasala, wanda kuma zai kawo cikas ga lafiyar mutum da kuma kwazonsa wajen ibada.

Hanyoyin kula da lafiya a cikin Ramadan
Kula da kai a lokacin azumin Ramadan bai takaita ga kiyaye abincin da ake ci kadai ba. Bacci na bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kula da lafiya kuma yana da kyau sosai a lokacin azumin Ramadan saboda lokaci ne da ake katse bacci domin yin sahur da kuma gudanar da ibada.

Yana da kyau a kiyaye bin salo daya wajen zabar lokacin bacci da kuma tashi domin ibada daga farko har karshen watan. Hakan zai sa a iya samun wadataccen bacci.

Gudanar da wasu ayyuka masu bukatar motsa jiki da rana wata hanya ce ta samun kuzari da motsa sassan jiki a lokacin azumi.

Mutum zai iya yin tattaki maras nisa sosai, ko wani wasan motsa jiki duk dai domin warware gabbai.

Mutane masu dabi’ar shan shayi da gahawa za su iya fama da ciwon kai da gajiya da rana saboda lokacin ne sinadarin caffeine da suka sha a cikin shayin yake barin jikin su, amma mafi yawa suna komawa daidai bayan mako guda, lokacin jiki ya fara sabawa.

Abu mafi muhimmanci dai shi ne mutum ya kiyaye alamomin da jikinsa ke bayarwa ya kuma dage wajen bin hanyoyin da zai su daidaita yanayin domin samun koshin lafiya.

A huta a lokacin da aka ji gajiya kuma a daina yin ayyukan da suka fi karfin jikin mutum, musamman da rana.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...