Jagoranci Nagari: Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yabawa Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar

Date:

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comr. Aminu Abdussalam, ya yabawa shugaban ma’aikatan jihar Alh. Musa Abdullahi, saboda gudunnawar da yake bayarwa wajen tafiyar da harkokin ci gaban ma’aikatan gwamnati a jihar.

Yabon ya zo ne a yayin wani taron da aka gudanar inda Alh. Musa Abdullahi ya samu karramawa daga al’ummar karamar hukumar Kiru bisa irin gudunmawar da yake baiwa karamar hukumar da ma’aikatan jihar Kano baki daya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shuaibu ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24 a ranar Lahadi.

Yadda Kalaman Abba Hikima akan Gwamnatin Kano suka tada kura a dandalin sada zumunta

A cewar Ibrahim, mataimakin gwamnan ya jaddada cewa nadin nasa na shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar kano nasara ce, da take da nasaba da gaskiya da rikon amanar sa wanda kuma al’ummar sa sun tabbatar da hakan.

Da yake yake bayani akan sa, Gwarzo ya bayyana Abdullahi Musa a matsayin jajirtacce Wanda yake da gogewa a harkokin aikin gwamnati da Siyasa, yace shugaban ma’aikatan jarumi ne abokin tafiya a kowanne hali.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa ya karfafawa Abdullahi gwiwa da ya dawo fagen siyasa don magance kalubalen da ke faruwa a Kiru da al’ummomin da ke kewaye, wanda hakan ya haifar da sakamako mai kyau ga karamar hukumar Kiru.

Yadda za ku kula da kanku a lokacin azumin Ramadan

Ya kuma bayyana amincewa da yadda Abdullahi yake jagorantar ma’aikatan gwamnati a jihar Kano, inda ya ce Abdullahi yana amfani da kwarewarsa wajen bunkasa duk wuri da aka tura shi.

Gwarzo ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana da kyakkyawan yakinin Abdullahi Musa zai sake fasalin hukumar ma’aikata ta jihar Kano.

Yayin da yake mika sakon fatan alheri ga Abdullahi, mataimakin gwamnan ya karfafa gwiwar matasa masu aiki a ma’aikatu daban-daban a fadin jihar da su yi koyi da irin jagoranci nagari domin samun ci gaba a harkokinsu.

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta dukufa wajen ganin ta ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi ga al’ummar jihar kamar yadda ta faro tun hawansa mulki.

Kwamaret Gwarzo ya kammala Bayanin nasa da neman goyon baya da addu’o’in al’ummar jihar Kano, inda ya jaddada mahimmancin hadin kai wajen ci gaban jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...