Ramadan: Azumin bana zai zo wa ƴan Nijeriya da tsanani – Shettima

Date:

 

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na sane da cewa azumin watan Ramadan mai gabatowa zai zo da kalubale masu tsanani ga akasarin ‘yan Najeriya saboda sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bullo da su.

Ya ce manufofin tattalin arziki da ake ɓullo da su na zuwa da kalubale da matsaloli, wanda zai zama “mafi tsanani ga talakawa.”

Daily Nigerian ta rawaito Shettima ya bayyana haka ne a yayin taron lacca karo na 29 na gabanin watan Ramadan da daliban jami’ar Legas suka shirya a Legas.

Kar Ku Rika Biyan Kudin Gyaran Transfoma —Kamfanin JED

Shettima, wanda mashawarcinsa na musamman kan harkokin siyasa, Hakeem Baba Ahmed ya wakilta, ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kalubalen da tattalin arzikin kasa a halin yanzu cikin “nutsuwa”.

Ya ce: “Shugabancin Shugaba Tinubu ya gane cewa wannan watan Ramadan zai zo da kalubale masu tsanani ga yawancin ‘yan Najeriya.

Ramadan: Sarkin Kano ya bukaci ‘yan kasuwa da su rage farashin kayan abinci

“Hanyar zuwa inda muke a yau tana da tsayi kuma tana cike da kalubaloli da kuma kasawa mai ban tausayi don gina babbanlr damarmu.

“Sakamakon abubuwan da suka faru a baya su ne ainihin abubuwan da muke fuskanta a yau, kamar hauhawar tsadar rayuwa da kuma rashin amincewa da yunƙurin kawo ci gaba.

“Mu tuna cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala yana jarrabar bayinSa da sauki da kuma kunci, kuma yana rokonmu da mu roke shi ya yaye mana kunci, da horo a lokutan yalwa.

“Muna fatan Allah Ya nuna mana azumin watan Ramadan kuma Ya karbi ibadar mu,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...