Daga Halima Musa Sabaru
Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu ta umurci hukumar Hisbah ta jihar Kano da hukumar kula da asibitocin jihar Kano da su ba da damar lauyoyin Murja Ibrahim Kunya su ganta.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Kotun Shari’ar Musulunci dake kwana hudu a zaman ta na karshe, ta bada umarnin kai Murja kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiya ƙwaƙwalwarta.
Wadanda aka yi karar su ne kwamishinan Shari’a jihar Kano, alƙalin kotun Shari’ar Musulunci dake Kwana hudu Malam Nura Yusuf Ahmed, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, hukumar kula da asibitocin jihar Kano, asibitin masu tabin hankali na tarayya dake Dawanau.
Gaskiyar Magana Kan Batun Sukar Aiyukan Hukumar Hisbah da Gwamnan Kano Yayi
Murja a cikin wata takarda da lauyanta ya gabatar, ta roki kotu da ta umarci wadanda ake kara na 4 da na 5 da su ba ta dama a rika ganin wacce Murja matukar bukatar hakan ta taso ba tare da wata matsala ba.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bukatar Murja Kunya da lauyanta.
Kotun ta kuma umurci wanda ake kara na 5 (Hukumar Kula da Asibitin Jihar Kano) da ta bai wa mai lauyan Murja kunya kwafin rahoton lafiyar kwakwalwar da aka yi mata.
Da dumi-dumi Sheikh Daurawa Ya Bayyana Dalilan sa na Yin Murabus Daga Kwamandan Hisbah ta Kano
Babbar kotun ta kuma umurci wanda ake kara na 2 ( alƙalin kotun Shari’ar Musulunci dake kwana hudu) da ya dakatar da ci gaba da gudanar da shari’ar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci Shari’ar dake gaban babbar kotun sannan ta bayar da kwafin gaskiya na shari’ar ga lauyan wanda ya shigar da kara.
Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 20/03/2024 domin jin asalin sammacin.
Al’amarin Murja Ibrahim kunya dai ya janyo cheche-ku-ce wanda ake ganin ita ce ta silar da ta sanya Kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye aikinsa a ranar wannan Juma’ar, bayan wasu kalamai da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayin inda ya soki salon yadda hukumar hizbah take gudanar da aiyukan ta na kawar da badala.