Yadda kamfanonin Kirifto ta Haddasa Tashin Farashin Dala a Nigeria

Date:

Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar hana kamfanin kirifto na Binance da sauran kamfanonin hada-hadar kuɗaɗen intanet yin hada-hada da kuɗin ƙasar, domin dakatar da abin da ta kira ‘yawaitar’ tashin farashin kuɗin ƙasar waje.

Wannan na zuwa ne sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kuɗin ƙasar waje ke yi a Najeriya, inda wasu ke zargin kamfanin Binance da sauran kamfanonin kuɗin intanet da yin uwa da makarɓiya wajen saka farashin dalar.

Da dama daga cikin ‘yan ƙasar na zargin cewa masu hada-hadar kuɗin kan duba shafin Binance da ake sabunta bayanai a kowace rana domin sanin farashin da za sayar da kudin kasar wajen.

Yawaitar faduwar darajar kuɗin Najeriya a baya-bayan nan na ci gaba da haddasa fargaba a zukatan ‘yan ƙasar, inda farashin kayayyaki ke cigaba tashin gawauron zabo, lamarin da ya jefa ‘yan kasar da dama cikin mawuyacin hali.

A ranar Labara dai an sayar da dala kan 1,800 a kasuwannin bayan fage.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha cewa tana ɗaukar matakan da suka dace don magance karyewar darajar kuɗin ƙasar.

A kokarinta magance matsalar gwamnatin ƙasar cikin watan Yulin 2023, ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen daidata kasuwa hada-hadar kuɗaɗen wajen.

Sannan a watan Agustan 2023, babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya karɓo bashin dala biliyan uku daga bankin Afrexim da zai biya da man fetur, domin tallafa wa gwamnatin ƙasar wajen daidaita farashin naira a ƙoƙarinta na cimma burin gwamnati.

Haka ma a watan Janairun 2024, babban bankin ƙasar, CBN ya ware kusan dala miliyan 61.64 domin warware bashin da kamfanonin jiragen waje ke bin ƙasar .

Ga kuma tarin samame da jami’an hukumar EFCC ke kai wa ‘yan kasuwar chanji, duk dai da nufin daidaita farashin kuɗin ƙasar waje a faɗin Najeriya.

To sai dai duk da waɗannan matakai da gwamnatin ƙasar ta dauka da alama kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Shi ne yanzu gwamnatin ke tunanin ɗaukar matakan rufe kamfanonin hada-hadar kuɗin kirifto, da nufin magance matsalar.

Gwamnatin ta ce ta samu bayanan cewa masu yaɗa jita-jita da masu almundahanar kuɗi na amfani da kamfanonin wajen aikata laifukansu.

Hukumomin ƙasar sun ce laifukan da ake aikatawa a shafukan kamfanonin kirifton su ke ƙara ta’azzara tashin farashin kuɗin kasar wajen tare da karyewar darajar kuɗin kasar wato naira.

Mene ne kamfanin Binance?

Muhammad Inuwa Aliyu wani masanin hada-hadar kuɗin kirifto a Najeriya ya ce Binace wani dandali ne da ake hada-hadar kuɗin intanet a duniya.

Kamfanin ya kasance ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke hada-hadar kuɗin intanet na duniya.

Masanin ya ce kamfanin Binance shi ne kan gaba wajen hada-hadar kuɗin intanet a duniya idan aka kwatanta da takwarorinsa irin su Bitcoin da sauransu.

A ina kamfanin Binance yake?

Changpeng Zhao ne ya samar da kamfanin ‘Binance Holdings Ltd’ a shekarar 2017.

An kuma fara buɗe kamfanin a ƙasar China, sannan ya koma Japan bayan da gwamnatin China ta ɓullo da matakan takaita ayyukan kamfanonin kirifto a ƙasar.

Sannan daga baya kamfanin ya fice daga Japan inda ya koma ƙasar Malta.

A shekarar 2021, hukumar shari’ar Amurka da hukumar tara kuɗin shiga ta ƙasar suka shigar da ƙarar kamfanin kan zarge-zargen laifukan haraji da halasta kuɗin haram.

Yaya kamfanin ke aiki?

Kamfanin Binance da na wani tsari da masu amfanin da shi ke buɗe asusun ajiyar kuɗin Intanet wanda da shi ne ake hada-hadar kuɗaɗen intanet a shafin.

Binance na amfani da kuɗaɗen da ake kira USDT wanda da shi ne ake hada-hadar kuɗin intanet shafin.

Kamfanin ya bai wa kuɗin kowace ƙasa daraja gwargwadon bukatar kuɗin shafin.

A shafin Binance babu iyakar kuɗin da za a iya tura wa mutum, saɓanin yadda tsarin Najeriya yake na dala 10,000 zuwa ƙasar waje, kamar yadda masanin ya yi bayani.

Ta yaya kamfanin Binance ke kayyade farashin dala?

kuɗin ƙasar zai farfaɗo a kamfanin Binance.

In kuma kamfanin ya ƙi amincewa da lalubo hanyoyin warware matsalar da gwamnatin Najeriya to gwamnati ta ce za ta yi ƙarar kamfanin domin ta cire naira a tsarinsa.

”A yau idan aka cire naira a cikin hada-hadar Binance, ina mai tabbatar maka da cewa kamfanin sai ya girgiza, saboda yadda ‘yan Najeriya ke hada-hada a kamfanin”.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar cigaban Ilimi da gyaran tarbiya ta unguwar zango ta shirya taron kan tarbiyya da tsaro

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malami a jami'ar Bayero dake...

Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da...

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...