DSS ta gargaɗi kungiyar Kwadago kan ƙudurinta na shirya zanga-zanga

Date:

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta janye ƙudurinta na shirya zanga-zangar gama gari domin samun zaman lafiya a Najeriya.

NLC ta tsara shiga yajin aikin ranar 27 da 28 ga watan Fabarairu a wasu yankunan ƙasar domin nuna rashin jin daɗinta ga halin matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke fuskanta da wasu matsaloli.

Wannan ya zo ne yayin da kwamishinan ƴan sanda a Abuja, CP Ben Igweh cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, ya ce rundunarsa ba ta da masaniya kan zanga-zangar da ake shirin yi a Abuja.

Yanzu-yanzu: Jami’an EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar Wapa

Sanarwar ta DSS ɗauke da sa hannun Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ta ce DSS ta samu labarin akwai wasu mutane da ke shirin yin amfani da zanga-zangar wajen tayar da husuma da kuma rikici.

Sanarwar ta ce “an ankarar da mu game da shirin da ƙungiyar ƙwadago ke yi na gudanar da zanga-zanga. Yayin da hukumar ta ce haƙƙin ƴan ƙwadago ne su yi zanga-zanga sai dai ta yi kira ga ƙungiyar ta soke shirin domin zaman lafiyar al’umma.

 

“DSS ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin su tattauna a maimakon yin abin da ka iya tayar da hankali. DSS ta ce ta samu bayanai cewa akwai wasu da ke son yin amfani da damar wajen janyo matsala da tashin hankali. Lamarin, ba tantama zai ƙara dagula yanayi da halin da ake ciki a sassan ƙasar.

Mun kammala bincike kan harin Tudun Biri – Rundunar sojin Najeriya

“Abin da aka sani ne cewa gwamnati a matakai daban-daban tana ƙoƙarin warware matsalolin tattalin arziki a don haka, a ƙara ba su dama. Zuwa yanzu, hukumomin da suka dace na aiki ba dare ba rana tare da masu ruwa da tsaki domin bijiro da dabarun magance ƙalubalen da ake fuskanta. A don haka a basu dama su magance matsalolin da ake fuskanta.

DSS ta ce ya kamata masu son yin amfani da damar su sake tunani ganin cewa karkata ga irin waɗan nan munanan tunane-tunane ka iya kawo maƙarƙashiya ga zaman lafiya.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...