Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta ce bata da hannu a sakin tauraruwar TikTok Murja Ibrahim kunya, wadda aka sake ta daga gidan yari bayan hukumar Hisbah ta jihar ta gurfanar da ita a gaban kotu.
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan zargin karya da ake ta yadawa a cikin al’umma musamman a kafafen sada zumunta na zamani inda ake Zargin gwamnatin tana da hannu a sakin fitacciyar ‘yar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Akwai lauje sakin tuhumamme tsakanin Gwamnati, Banggaren Sharia da Hisbah
“Wannan zage-zage da kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, zargi ne kawai da wasu marasa kishin kano suka yi domin bata sunan gwamnati da mutuncin Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf”. A cewar sanarwar
Sanarwar tace gwamnatin jiha tana sane da tanadin da kundin tsarin mulkin kasar nan yayi na raba iko ga wanne bangare na mulkin dimokaradiyya, wadanda suka hadar da bangaren shari’a, majalisa da kuma na zartaswa.
Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano ta Magantu Kan Bacewar Murjar Kunya a Gidan Yari
“Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta taba yin wani da zai kawo cikas ko zubar da kimar wani bangare ba cikin bangarorin nan uku. Gwamnati tana sane da cewa batun Murja yana gaban kotu don haka bazata yi katsalandan ta kowace hanya ba wajen hana kotu yin aikin ta”.
Idan dai ba a manta ba gwamnati ta san Murja Kunya ta gurfana a gaban wata babba Kotun Shari’a ta da ke Kwanar Hudu a karamar Hukumar Nassarawa bisa zargin ta da yada wasu munanan faifan bidiyo a dandalin sada zumunta inda kotu ta bayar da umarnin a tsare ta zuwa ranar Talata, 20 ga Fabrairu, 2023 bayan ta saurari bukatar neman belin ta.
” Sai dai labari ya zo wa gwamnati cewa an sake samun ta da wani sabon zargi da ake yi mata wanda ya sa jami’an tsaro suka fitar da ita domin gudanar da bincike. Duk da haka kotu zata cigaba da sauraren shari’arta har zuwa matakin karshe da kotu ta yanke”.
Sanarwar tace ana kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnatin jihar, wanda wasu ke kokarin bata mata suna tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar dokoki da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.