Kotu ta Yanke Wa Ramla Yar TikTok Hukunci Bisa Laifuka Uku

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kotun shari’ar addinin Muslunci dake zaman ta a hukumar hisbah ta jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Malam Sani Tamim Sani Hausawa, ta yanke wa yar TikTok din nan Ramlat Muhammad hukuncin daurin watanni 7 a gidan yari .

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da y gabata ne hukumar Hisbah ta jihar kano ta gurfanar da matashiyar a gaban kotu, saboda wasu kalamai da ta yi na cewa ita yar madigo ce kuma duk namijin da zai aureta sai ta bata damar auro tata Matar.

Mai Shari’a Malam Sani Tamim yace kotun ta sami Ramlat Muhammad wadda akewa lakabi da Princess da laifin badala, fitsara da kuma yawon banza.

Akwai lauje sakin tuhumamme tsakanin Gwamnati, Banggaren Sharia da Hisbah

A yammacin ranar litini 19 ga Fabrairu 2024, Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa ya yanke wa Ramlat hukuncin dauri na tsawon watanni bakwai da zabin biyan tarar Naira 50,000.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da ita kan laifuka kamar haka:

Fitsara da rashin tarbiyya da yada ɓaɗala, da yawon banza wanda ya saba da sashe na 389 na dokar Shari’ar Musulunci ta jihar kano.

A tuhumar farko alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Ya Magantu Kan Sakin Murja Kunya Daga Kurkuku

Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a ko zabin tara na Naira 20,000.

A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata guda babu zabin tara.

Idan za’a iya tunawa dama tun a hannun jami’an hukumar Hisbah ta jihar kano Ramat ta amsa laifinta tare da neman ayi mata sassauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...