An tattauna yadda za’a samar da sauki yayin aure a karamar hukumar Bagwai

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

 

Kungiyar jama’atu Nasril Islam reshe Karamar hukumar Bagwai ta shirya taro masu ruwa da tsaki domin kawo masalaha yayi gudanar aure a dukkan fadi Karamar hukumar ta Bagwai.

Madawakin Bichi hakimin na Karamar hukumar ta Bagwai Alh Nura Shehu Ahmad ne ya jagoranci taron .

Masu ruwa da tsaki sun hada da dagatai, masu Unguwani da Limamai manyan mallamai addinin Musulunci dake fadin ta Karamar hukumar ta Bagwai.

Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano ta Magantu Kan Bacewar Murjar Kunya a Gidan Yari

A wata makalar daya gabatar akan Mahimmanci Aure tsakani Mijin da Mata a Shari’ar musulunci da Kuma waya kamata ya Samar da kayan daki a Sharia musulunci yayi gudanar da aure Gabatar Babban Limamin garin Kiyawa dake Karamar hukumar ta Bagwai Mallam BILYAMINU Abubakar yace ayyoyin Qur’an da hadisan manzo Allah (s a w) nauyi da Sharia musulunci ta daurawa Ma’aurata.

Kano: NAFDAC da Gargaɗi Kamfanoni Game da Yan Kasuwar Magani na Sabon Gari

Dan Majalisar Koli na Kwamiti Jama’atu Nasril Islam na Karamar hukumar ta Bagwai Wanda Kuma shi ne Na’ibi Limamin Juma’a na Karamar hukumar Bagwai Mallam Sani Musa Bagwai ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tattauna hanyoyi Samar da masalaha tsakani bangarorin masu masu aure a fadi Karamar hukumar ta Bagwai.

Mallam Aminu Yusuf Bagwai shi ne wakilin Kungiyar Kadiriya a Kwamiti ya bayan Mahimmanci bin tsarin addini musulunci yayi gudanar da aure, Inda yace matukar akabi tsari da Musulunci ya zo da shi wajen aure za’a sami saukin wahalhalun da aka fuskanta.

Yace Kwamiti na Jama’atu nasril Islam zai kawo dedeto a dukkan sukar aure a fadi Karamar hukumar ta Bagwai.

Taro ya Sami halartar dukkan dagatai masu Unguwani da Limamai dake Karamar hukumar ta Bagwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...