Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Jarumar kannywood Amal Umar ta bayyana cewa babu wata alaka ta soyayya tsakaninta da mawaki Umar M Shariff sai dai kyakykyawar fahimtar juna dake tsakanin su.
Jarumar ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ta yi da shafin BBC Hausa.
” Muna da kyakykyawar fahimtar juna da Umar M Shariff, kuma mun shaku sosai watakila hakan ce tasa ake tunanin muna soyayya”.
Kotu a Kano ta dauki mataki kan hukumar Hisbah, bayan da wasu masu otel sukai karar ta
Da aka tambayeta matsayin jaruma Maryam Yahaya a wajenta , Amal Umar ta ce Maryam din kawarta da suke da fahimtar juna a baya.
” Maryam Yahaya a baya bani da kawa kamarta , amma yanzu mun dan yi nisa saboda yanayin aikin mu da kuma girma da muka kara yi, amma ba fada mukai ba”. A cewar Amal Umar.