Matakin da CBN ya Dauka Kokari ne Na Durgusar da Arewa – Kungiyar NRO

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kungiyar farfado da Arewacin Nigeria (Northern Reform Organization) ta ce bata yi mamakin kin karbar shawarar da suka bayaiwa babban bankin Nigeria CBN ba na dakatar da shirinsa na dauke wasu sassan helkwatar bankin daga Abuja zuwa jihar Lagos .

“Kin karbar shawarwarin mu dana sauran kungiyoyi da daidaikun yan Arewa ya tabbatar mana da yunkurin da ake yi na Aiwatar da wata manufa ta son kai, don haka muna kira da babbar murya da a gagguta janye waccan manufa, a dawo da wadancan sassa Inda suke”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Yusuf Gude da Daraktan yada labaran kungiyar Mahmud Adnan Audi suka sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana

” Muna kira ga dukkan wakilanmu a matakai daban-daban na al’umma musamman gwamnati da su farka
domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma tabbatar da cewa an hana duk wani da zai zama zalunci ga arewa da sauran sassan kasar nan”. A cewar sanarwar

“A kowanne lokaci Arewa Ake so a mayar kurar bayan ta hanyar dakile duk wani cigaba da take da shi ko wanda zai zo mata, don haka dole mu Farka mu kare kima da martabar arewa domin ta sami cigaba ta kowanne fanni na rayuwa”.

Kotu ta gindaya sharudda 2 kafin bada belin Danbilki Kwamanda

Sanarwar tace da gangan aka kirkirarwa arewa ‘yan fashi, masu tayar da kayar baya, duk da nufin gurgunta aikin gona, ilimi, kasuwanci, masana’antu, da sauransu. “dole ne a kalli wadancan abubuwa da idon basira don a magance su don mu sami cigaban da muke fata.

“Rashin Hasken wutar lantarki ya Mambilla, kamfanin sarrafa karfafa na Ajaokuta, yashe kogin Niger da dai sauransu su ne abubunwan da ya kamata wannan gwamnatin ta mayar da hankali akan su don kammala su, bawai wani abu daban ba, Wanda zai jawowa Arewacin Nigeria koma baya”.

Kungiyar ta farfado da Arewacin Nigeria ta kuma shawarci Arewa da ta fito da tsare-tsare masu gajere da dogo zango l don hada kai da gwamnatocin jihohi daban-daban, kungiyoyi masu zaman kansu, da dai sauransu don ciyar da yankin mu gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...