Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce mota ta buge wani mutum da ya yi kwacen waya yayin da ya sheka a guje domin tsallaka titi a cikin birnin na Kano.
Bayan mota ta buge wani mutum da ya zare makami (dan buda) ya kwaci wayar wata mata, an gano cewa kashin bayansa ya karye kuma kansa ya fashe”, in ji kakakin ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa.
Hukuncin Kotun Ƙoli: Gwamnan Kano Abba Ya Magantu Kan Alakar Nasarar sa da Tinubu
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi da maraice.
“Yanzu na samu rahoto daga Zoo Road cewa wani ya zare danbida ya kwaci wayar wata mata. Yana tsallaka titi mota ta kade shi. Ana bukatar mu kai shi asibiti,” in ji Abdullahi Kiyawa.
Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC a Kano Ta Magantu Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli
Sai dai daga bisani kakakin ‘yan sandan na Kano ya sake wallafa wani sako da ya nuna cewa mutumin da ya kwaci wayar yana cikin mummunan yanayi.
“Bayan Mun Kai shi asibiti likitoci sun tabbatar da cewa kashin bayan wanda ya kwaci wayar ya karye sakamakon bugewar da Mota ta yi masa”.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sha kama masu kwacen waya tana gurfanar da su a gaban kuliya.