Yadda Gobara ta Hallaka Miji da Mata da Yaƴansu 5 a Kano

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Wani magidanci mai suna Shuaibu Iliyasu da matarsa Binta da kuma ƴaƴansu biyar sun rasu a wata gobara da ta tashi tsakar dare a unguwar Tudun Wada a ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

 

Mazauna unguwar sun tabbatarwa Daily Nigerian cewa wutar ta tashi ne bayan ƙarfe 12 na dare a yayin da matan ke tsaka da barci.

Yadda Mota ta Take Wani Mai Kwace Waya da Makami a Kano – ‘Yan sanda

A cewar wani mazaunin unguwar, Malam Idi Maikatako, wutar ta tashi ne tun misalin bayan ƙarfe 12 na dare, inda ya yi tsammanin cewa kawo wutar lantarki ne ya haifar da tararratsin wuta da ya kai ga tashin gobarar.

 

Ya kara da cewa da jin afkuwar lamarin, tuni makota su ka shiga gidan domin kawo ɗauki, inda kafin ayi aune, 7 daga mutanen da ke barci a dakin sun rasu, sai yau ya ɗaya da ta rage, wacce aka garzaya da ita asibiti.

Kotun Ƙoli Ta Jingine Hukunci Kan Zaɓen Gwamnan Ribas

Jami’an hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Kano, PFS Saminu Yusif ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon hayakin da ya cika dakin da su ke.

Ya ce sun karbi kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar, Ibrahim Sani da misalin karfe 12:25 na dare cewa wasu ƴan daki daya su bakwai sun rasu sakamakon gobara.

Ya ce da jami’an su na unguwar Dakata su ka isa gidan, sai suka tarar tuni an kashe wutar kuma an fito da mamatan sannan an garzaya da ƴar daya till da ta rage zuwa asibiti.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika kashe duk wani soket na wuta idan za a kwanta domin kare faruwar haɗarin wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...