Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A ranar Litinin kotun koli ta jingine hukunci a karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Patrick Tonye-Cole, ya shigar kan nasarar da Gwamna Siminalayi Fubara ya samu.
Alkalan kotun biyar karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ne suka jingine hukunci kan karar bayan dukkan bangarorin da ke karar sun gabatar da bayanan su.
Yadda Mota ta Take Wani Mai Kwace Waya da Makami a Kano – ‘Yan sanda
Dan takarar na APC ya kuma ce Fubara bai cancanci tsayawa takara ba amma INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da zaben Fubara a matsayin gwamnan Ribas.
Hukuncin Kotun Ƙoli: Gwamnan Kano Abba Ya Magantu Kan Alakar Nasarar sa da Tinubu
Kotun ta yi watsi da karar da Tonye-Cole, ya shigar a kan Fubara, PDP da INEC.
Dan takarar na jam’iyyar APC ya bukaci kotu da ta umurci INEC da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ribas na watan Maris.
Sai dai kotun ta ce duk wadanda suka shigar da kara sun kasa tabbatar da zargin rashin bin dokar zabe.