‘Yan sanda a kano sun kama mutum 9 da laifin sayar da yara

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane tara da suka kware wajen safarar kananan yara da sace-sace da kuma sayar da kananan yaran.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar dake Bompai a Kano, ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike cikin asiri, inda aka gano cewa, wasu kungiyoyi dake safarar kananan yara a sassan jihohin Kano, Bauchi, Gombe, Legas, Delta, Anambra da Imo, aka kuma wargaza su.

Talla

Gumel ya ce an kubutar da mutane bakwai wadanda akasarinsu kanana ne daga hannun wadanda ake zargin.

Ta hanyar bincike mai zurfi da tawagar jami’an mu suka gudanar, muka gano ayyukan wadannan kungiyoyin masu aikata laifuka da suka shafe sama da shekaru 10 suna aiki,” inji shi.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Sauyawa Ma’aikatar Mata ta Jihar Suna

Kwamishinan ya bayyana cewa an sayar da wasu daga cikin yaran da aka ceto masu shekaru tsakanin uku zuwa takwas da aka ceto a tsakanin N300,000 zuwa N600,000 dangane da shekarun su.

“A yayin bincike an gano cewa, an sayar da wani da aka kashe mai suna Mohammed Iliya, wanda aka sace daga Bauchi amma aka canza sunansa zuwa Chidebere a Nnewi da ke jihar Anambra,” in ji Gumel.

Ina alfahari da Salon shugabancin ka , Tinubu ya fadawa Ganduje

Ya ce rundunar za ta hada kai da gwamnatin jihar kano domin tabbatar da ganin an dawo da dukkan yaran da aka sace lafiya tare da mika su ga ’yan uwansu na asali.

Kwamishinan ya tabbatar wa da jama’a cewa rundunar da ke karkashin sa ta samar da matakan tsaro domin kawo karshen matsalar gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...