Zargin fitar da kudade: Jam’iyyar APC ta Gargadi Gwamnatin Kano

Date:

Daga Aisha Muhammad Adam

 

Jam’iyyar APC ta koka kan shirin gwamnatin jihar Kano na kashe naira biliyan 8 na kudaden kananan hukumomi ba tare da wani dalili ba.

Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ranar Talata a Abuja.

Abdullahi Abbas ya bukaci kananan hukumomi da bankunan kasuwanci a jihar da su dakatar da aikin fitar da kudade ga gwamnatin jihar.

Talla

Ya ce hakan na faru ne saboda rashin tabbas na siyasa a jihar sakamakon hukuncin kotun koli da ake jira a kan zaben gwamna.

Abbas ya ce da alama wannan hakan ne ya sa gwamnatin NNPP ta karbe ayyukan kananan hukumomi domin yin almubazzaranci da kudadensu da suka haura Naira biliyan 8.

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Na’Abba ya rasu yana da shekaru 65

Ya ce jam’iyyar APC ta samu kwafin takardar amincewa daga ma’aikatar kananan hukumomi ta umurci kananan hukumomi 44 da su fitar da naira miliyan 101 kowannen su domin gina gada a Dan’Agundi da kuma naira miliyan 36 kowannen su don gina wata gadar Tal’udu.

“Wasikar amincewa, wacce aka aika zuwa ga shugabannin kananan hukumomi, an kuma aika da kwafin ta zuwa ga babban mai binciken kudi, masu binciken kudi na kananan hukumomi da dukkanin jami’an ma’aikatar shiyya da suna za ayi musu aiyuka.

Talla

Abbas ya ce gwamnatin NNPP ta cire tare da sanya sabbin daraktocin kula da ma’aikata (DPMs) da ma’aji domin cika wannan buri nata, don ganin ba a samu cikas ba wajen murde kananan hukumomin ba ta hanyar almubazzaranci da kudadensu.

Ya yi kira ga gwamnatin jam’iyyar NNPP da ta yi la’akari da muradun al’ummar jihar, inda ya ce matakin gudanar da irin wadannan ayyuka ya fuskanci kalubale tun daga ‘ya’yan jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...