Sanata Abdul’aziz Yari (APC-Zamfara) a jiya Talata ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da addu’o’in kawo karshen ƴan fashin jeji da masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a kasar nan.
Yari, wanda ke wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, ya yi wannan roko ne a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki na ‘yan siyasa 147 na Zamfara a gidansa da ke Talata-Mafara.

A cewarsa, addu’a ce kadai za ta iya magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta da sauran sassan kasar.
“Kalubalen tsaron da ake fama da shi a kasar nan na kara ta’azzara duk da matakan da gwamnati ta dauka na magance shi.
Muhimman Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Ghali Umar Na’Abba
“Abin takaici ne, ayyukan rashin tsaro sun kara zama ruwan dare a kullum a cikin al’ummominmu.

“Saboda haka, dole ne mu dage da addu’o’in neman taimakon Allah don kawo mafita mai dorewa a kan matsalar,” in ji shi.